Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Jaridar Premium times ta sami kofin sanarwan tabbatar da wannan labarin wanda ministan kiwon lafiya na kasar Dr. Osagie Ehanire ya sanya hannu a ranar 8 ga watan Dicemba shekara ta, 2021.
Ministan ya kuma kara da cewa hukumar NAFDAF mai kula da magunguna da abinci ta kasar zata dauki nauyin murkushe alluran wadanda suka lalace a cikin watan da ya gabata.
Labarin bai bayyana adadin alluran da suka lalace ba, ko kuma sunayensu, amma wata majiya wacce bata son a bayyana sonata ta fadawa kamfanin dillancin labaran Reuters kan cewa alluran na kamfanin AstraZeneca ne, wanda aka aikowa kasar ta hukumar COVAX. Amma ta ce adadin bai kai miliyon daya kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka bayyana ba.
Hukumar lafiya da duniya WHO dai ta bayyana cewa kasha 4% ne kacal daga dimbin al-ummar Najeriya wacce aka kiyasta ta kai miliyon 206 aka yiwa cikekken alluran riga kafin na cutar ta Covid 19 ya zuwa yanzu.
342/